Yau ne aka kaddamar da taro karo na biyar na dandalin tattaunawa a tsakanin jama'ar Sin da Afirka a birnin Chengdu na kasar Sin, inda Shugaban kasar Xi Jinping ya aika da sakon taya murnar kaddamar da taron
A cikin wasikar, Shugaba Xi ya nuna cewa, dandalin tattaunawa a tsakanin al'ummar Sin da Afirka wata muhimmiyar gada ce a tsakanin jama'ar bangarorin biyu. Tun bayan da aka kafa dandalin a watan Agusta na shekarar 2011, dandalin ya samu babban ci gaba bisa ka'idoji uku wadanda suka hada da "kara dankon zumunci a tsakanin jama'a, da inganta hadin gwiwa, da kokarin tabbatar da zaman lafiya a duniya". Dandalin ya kuma taka muhimmiyar rawa ga cudanya da hadin kai a tsakanin jama'ar Sin da Afirka.
Bugu da kari Xi ya jaddada cewa, ana daukar batun "tattara karfin jama'a don kara azama ga aminci da fahimta a tsakanin Sin da Afirka" a matsayin babban taken taron na bana, wanda zai inganta mu'amala da hadin kai a tsakanin jama'ar bangarorin biyu sosai.(Kande Gao)