Shugabannin biyu wadanda suka bayyana hakan a Litinin din nan, sun jinjinawa alakar diflomasiyyar kasashensu, wadda ta shafe shekaru sama da 47.
Da yake tsokaci game da hakan, shugaba Xi ya waiwayi ganawarsa da shugaba Kagame a birnin Beijing ta watan Maris na shekarar 2017, lokacin da suka cimma matsaya guda, game da burinsu na karfafa alaka da kawancen kasashensu, matakin da a cewar Xi zai taimaka wajen bunkasa ci gaban sassan biyu.
Ya ce Sin na da burin aiki tare da mahukuntan Rwanda, domin bunkasa kawance na gargajiya, wanda zai amfani kasahen biyu da ma al'ummun su, ya kuma bude wani sabon shafi a fannin hadin gwiwa da abota tsakanin sassan biyu.
Kaza lika Sin na maraba da shigar Rwanda shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya", tana kuma karfafar gwiwar 'yan kasuwarta, da su kara zuba jari a Rwanda, domin kara bunkasa zamanantar da masana'antun Afirka.
Shugaba Xi ya isa birnin Kigali, fadar mulkin kasar Rwanda a jiya Lahadi domin kaddamar da ziyararsa ta aiki a kasar. Wannan ne karo na farko da wani shugaban kasar Sin ya kai ziyara wannan kasar Afirka. (Saminu Hassan)