Yayin zantawar shugabannin biyu a Talatar nan, shugaba Xi Jinping da takwaran sa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, sun amince da bukatar karfafa musaya bisa matsayin koli, da fadada hadin gwiwa da amince a fannin siyasa, da daidaita tsare tsare, da bunkasa hadin kai da kara musaya tsakanin al'ummun su, ta yadda alakar sassan biyu za ta haifar da samakamo mai alfanu. (Saminu)