Tunanin Xi Jinping na yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ya kafa sabuwar alkibla ga kasar Sin
Kwanan baya ne, aka wallafa wani littafi mai suna "Nazari Kan Tunanin Xi Jinping Game Da Yin Gyare-gyare A Gida Da Bude Kofa Ga Kasashen Waje", wanda ya jawo hankalin gami da babban yabo daga bangarori daban-daban. Manazarta na ganin cewa, bana shekaru arba'in ke nan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bude kofarta ga kasashen ketare. Kana, yayin da ayyukan yin gyare-gyare a cikin gida da kasar Sin ke gudanarwa ke cikin wani muhimmin mataki, tunanin Xi ya kafa wata sabuwar alkibla ga ci gaban kasar a nan gaba. Hakika, Xi Jinping ya zama babban mai tsara fasalin ci gaban kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki.
Har wa yau, wannan littafi ya jawo hankalin kafafen yada labaran kasa da kasa. Jaridar Leadership ta Najeriya da jaridu da gidajen rediyo da talabijin na kasashen Rasha da Laos da Spaniya da Albaniya da Indiya da sauran wasu kafofin watsa labarai na Amurka da Birtaniya gami da Japan sun ruwaito rahotanni game da wallafa wannan littafin. (Murtala Zhang)