Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban rundunar askawarar kasar, ya bayyana hakan ne, cikin umarnin da ya bayar game da magance matsalar ambaliyar ruwa da aikin kai dauki ga wadanda bala'i ya shafa, sakamakon mamakon ruwan saman da ya yi barna a yankunan kasar da dama, lamarin da ya haddasa zaftarewr laka da tumbatsan koguna tun a watan Yuli.
Xi ya kuma bukaci kwamitocin jam'iyya da gwamnatocin wadannan yankunan, da su kasance masu daukar matakan da suka dace, su zage damtse wajen gudanar da aikin ceto, da rage jikkata, da kula da wadanda suka tsira daga bala'in da rage hasarar dukiyoyi yadda ya kamata. (Ibrahim)