Littafin ya samar da bayanai ne daga fannoni tara da suka hada da rike sabbin zarafin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da sa kaimin gyare-gyaren tsarin tattalin arziki ta bangaren samar da kayayyaki, da daidaita huldar da ke tsakanin kasuwanni da gwamnati, da raya kasa mai tsarin gurguzu da ke da karfin al'adu, da samar da tsarin kula da harkokin al'umma da raya kyakkyawar kasar Sin, da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da kuma kiyaye jagorancin jam'iyyar kwaminis a kan ayyukan yin gyare-gyare da bude kofa.
Babban mai tsara littafin, wanda kuma shi ne shugaban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, Shen Haixiong ya yi nuni da cewa, ra'ayoyin shugaba Xi Jinping game da yin gyare-gyare da bude kofa, alama ce ta sabon matsayin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kai ta fannin binciken ka'idojin yin gyare-gyare da bude kofa, wadanda kuma suka bayyana ainihin tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, tare da fadada nazarin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin. (Lubabatu)