Yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta dauki EU a matsayin wani karfi mai muhimmanci dake iya amfanawa yanayin duniya. Ya ce ya kamata bangarorin biyu, su raya dangantakar abota a dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare, da ci gaba da sa kaimi ga kafa dangantakar dake mai da hankali kan manyan fannoni hudu, da suka hada da tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa da yin kwaskwarima da inganta al'adu.
Mista Xi ya nuna cewa, a bana Sin ke cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje, inda ya ce kasar ta sanar da jerin tsare-tsarenta na bude kofarta ga kasashen waje, kuma za ta ci gaba da zurfafa yin kwaskwarima a gida da habaka bude kofa ga kasasen waje. Ya kara da cewa, Ya kamata Sin da Turai su kara hada kan juna saboda kiyaye tsarin bunkasar duniya na bai daya da kasancewar bangarori daban-daban a duniya, kana da kiyaye manufar gudanar da aiki tsakanin bangarori da dama da tsarin raya tattalin arzikin duniya na bude kofa bisa ka'idar yin ciniki cikin 'yanci.
A nasu bangaren, Tusk da Juncker sun bayyana godiya ga goyon bayan da Sin take bayarwa wajen raya nahiyar Turai, tare da fatan kara hadin kai da kasar Sin a fannoni daban-daban, da kara tutunbar juna cikin harkokin duniya. Sun ce EU da Sin na dukufa kan goyon bayan manufar tattaunawa tsakanin bangarori daban-daban da dokar kasa da kasa bisa tushen ka'ida, da kuma daidaita dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da kuma kyautata tsarin ciniki tsakanin bangarori da dama ta hanyar yin shawarwari. (Amina Xu)