Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tashi daga birnin Beijing a yau Alhamis, domin fara ziyarar aiki a hadaddiyar daular Larabawa, kana zai isa kasashen Senegal, da Rwanda, da Afirka ta kudu, inda zai kuma halarci taron koli na 10, na kungiyar BRICS da zai gudana a birnin Johannesburg. Shugaba Xi zai kuma gudanar da ziyarar sada zumunta a kasar Mauritius kafin dawowar sa nan birnin Beijing.
Shugaba Xi dai ya samu gayyata ne daga sarkin masarautar hadaddiyar daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, da shugaba kasar Senegal Macky Sall, da shugaban Rwanda Paul Kagame, da kuma na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa.(Saminu)