Xi Jinping ya yi nuni da cewa, manyan jam'iyyun siyasa shida na kudancin nahiyar Afirka muhimman jam'iyyun siyasa ne da suka taimaka ga samun 'yancin kan al'ummar kasa da raya tattalin arziki a yankin, wadanda suka hada kai wajen kafa cibiyar nazarin shugabanci ta Nyerere don kara raya jam'iyyunsu da inganta karfin gudanar da ayyukansu, hakan zai taimaka wajen samun ci gaban kasashen. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana son yin amfani da wannan dama wajen kara yin mu'amala da koyi da juna tare da jam'iyyun kasashen Afirka ciki har da jam'iyun siyasun shida don ganin an kafa tsarin cimma buri da Sin da Afirka ke fatan cimmawa tare da samar da gudummawa wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa a duniya baki daya. (Zainab)