Karin kamfanonin kasashen waje sun zabi kasar Sin don gabatar da kararsu a fannin tabbatar da ikon mallakar ilmi, wannan ya shaida cewa, sun amince da nuna imani ga tsarin tabbatar da ikon mallakar ilmi na kasar Sin.
Gwamnatin kasar Amurka sun tada yakin ciniki da kasar Sin a dalilin rashin tabbatar da ikon mallakar ilmi a kasar Sin, burinta shi ne hana bunkasuwar kimiyya da fasaha da tattalin arzikin kasar Sin. Game da yakin ciniki da za a fara, Sin ba ta son yin yakin, kana ba ta jin tsoron yin yakin, tilas ne za ta mayar da martani. Haka zalika kuma, Sin za ta ci gaba da tabbatar da ikon mallakar ilmi, tare da ci gaba da samun bunkasuwa a fannin kimiyya da fasaha. (Zainab)