Sabbin manufofin za su shafi yankunan ciniki mara shinge na lardin Guandong dake kudanci kasar da lardin Fujian na kudu maso gabashi tare da yankunan kasuwanci na arewa maso gabas da suka hada da na lardunan Jilin da gabashin Jiangsu da Zhejiang da kuma Fujian.
Manufofin da aka yi wa gyaran fuska, za su tabbatar da gaggauta hanyoyin neman izinin zama na dindindin ga baki da suka samu yabo daga wajen Gwamnati da samar da tallafi ga dalibai baki dake da niyyar fara kasuwanci da gaggauta samar da visa da hanyoyin samun izinin zama ga Sinawa dake kasashen waje da dai sauran hanyoyi masu sauki.
A shekarar 2016, ma'aikatar ta samar da wasu jerin manufofi ga baki dake aiki a yankunan cinikayya marasa shinge a lardunan Guangdong da Fujian. A kuma farkon shekarar nan ne, aka aiwatar da 7 daga cikin manufofin a Karin wasu yankunan kasuwanci dake fadin kasar. (Fa'iza Mustapha)