A jiya ne shugaban Amurka Donald Trump, ya rattaba hannu kan wata takardar da umurci Amurka ta janye daga yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen yankin Fasifik wato TPP a Turance.
Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta shaida wa taron manema labaru a yau Talata cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan samun moriyar juna da nasara tare, da kuma martaba yarjejeniyar ciniki ba tare da shinge ba a tsakanin shiyya-shiyya. Kasar Sin tana son hada kai da sassa daban daban domin magance matsalolin da duniya ke fuskanta a halin yanzu da kuma neman samun ci gaba da wadata a duk duniya baki daya. (Tasallah Yuan)