Mr. Cui ya fadi hakan ne a yayin da yake hira da Bill Sternberg babban editan jaridar USA Today, a game da yadda gwamnatin kasar Amurka ke sanya kudin kwastan masu yawa a kan kayayyakin kasar Sin.
Mr. Cui ya ce, Sin da Amurka suna samun moriyar juna daga huldar tattalin arziki da cinikayya da juna. Duk da matsalar da ake iya fuskanta a kan wasu batutuwa, amma kasashen biyu na alaka da juna sosai ta fannin tattalin arziki, misali yanzu da wuya mu tabbatar da cewa wani kaya kasar Sin ce ta samar ko kuma Amurka ta samar.
Mr. Cui Tiankai ya kara da cewa, kamata ya yi a daidaita matsalolin bisa tsarin cinikayya da ya hada da hukumar cinikayya ta duniya(WTO).
Daga karshe, Mr.Cui Tiankai ya ce, kasashen Sin da Amurka na kara fuskantar cikas da batutuwan siyasa ke kawo wa harkokin cinikayyarsu, abin da kuma ya jawo hankalinsu duka, kuma matakan kariyar ciniki da aka dauka ba za su taimaka ga daidaita matsalolin da aka fuskanta ta fannonin tattalin arziki da zaman al'umma ba.(Lubabatu)