A yau ne, Shen Danyang, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, duk yadda makomar yarjejeniyar TPP ta kasance a nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da yin gyare-gyare a cikin gida da kuma bude kofarta ga kasashen ketare. Haka kuma za ta yi ciniki a tsakanin sassa biyu da ma tsakanin sassa daban daban ba tare da wata matsala, a kokarin ba da gudummowa wajen saukaka harkokin ciniki a duniya.
A kwanan baya ne, Donald Trump, shugaban kasar Amurka mai jiran gado ya gabatar da manufofin da zai kaddamar a cikin kwanaki 100 bayan da ya hau kujerar mulkin kasar, ciki had da sanarwar neman ficewa daga yarjejeniyar cinikayya ta TPP. (Tasallah)