Ra'ayin kafofin watsa labaru dangane da shawarwarin da ake yi tsakanin Sin da Amurka
Daga ranar 2 zuwa ta 3 ga watan da muke ciki, bangarorin Sin da Amurka sun samu ci gaba a shawarwarin da suke yi dangane da batun cinikayyar kasashen 2. Bisa wannan yanayin da ake ciki ne, jardar Economic Daily da jardar Global Times na kasar Sin sun wallafa bayanan dake cewa, manufar gyare-gyare da bude kofa da yunkurin habaka bukatun cikin gida wasu manyan tsare-tsare ne na kasar Sin, wadanda ba za ta canza su ba. Saboda haka ya kamata bangarorin Sin da Amukra su yi amfani da tsare-tsaren wajen samar da sakamako a shawarwarin da suke gudanarwa. Sai dai bai kamata ba bangaren Amurka ya dauki wani ra'ayin da bai dace da hakikanin yanayin da ake ciki ba.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku