Kwanan baya, majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta kaddamar da rahotonta dangane da yadda ake kare hakkin dan Adam a kasashen duniya a shekarar 2017, inda ta sake zargin kasar Sin kan hakkin dan Adam.
Dangane da lamarin, Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, yunkurin Amurka na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin ta irin wannan hanya, tare da neman kawo illa ga bunkasuwar kasar Sin, bai samu nasara ba a baya, kuma yanzu ma hakar ta ba za ta cimma ruwa ba.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin ta yarda da yin tattaunawa da mu'amala a tsakanin kasashen duniya kan batun kare hakkin dan Adam bisa ka'idar zaman daidai wa daida da girmama juna, a kokarin yin koyi da juna da samun ci gaba tare. A sa'i daya kuma, yawancin kasashen duniya, ciki had da Sin, ba sa goyon bayan sanya siyasa kan batun da ya shafi hakkin dan Adam. (Tasallah Yuan)