in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JPMorgan: Kara bude kofofin Sin na jawo karin jari daga sassan duniya
2018-05-07 20:21:30 cri

Babban manaja, kuma mataimakin shugaban bankin JPMorgan na Amurka reshen yankin Asiya da Pasifik Jing Ulrich, ya ce kara bude kofa da kasar Sin ke yi a yanzu haka, na dada jawowa kasar jarin waje daga dukkanin sassan duniya.

Mr. Ulrich ta ce masu zuba jari na kara shiga hada hadar kasuwanci, da bunkasa kasuwannin kasar Sin. Ya ce kyawawan matakai na gudanar da kasuwanci da mahukuntan Sin ke dauka, kamar rage wasu haraji, da saukaka samun takardun izini, na kara baiwa masu zuba jari kuzari na shiga kasuwannin kasar.

A farko wannan shekara ta 2018 ne dai aka fara aiwatar da karin matakan saukaka shiga kasuwannin Sin, matakin da ya zo a gabar da kasar ke ciki shekaru 40 da fara aiwatar da manufofin ta na bude kofa ga kasashen ketare. Ana kuma sa ran za a kara rage harajin shigo da ababen hawa, da rage shinge kan kamfanonin dake kirar su, da sashen samar da kudade.

Kaza lika za a sanya hannayen jarin kasar Sin rukunin A, cikin tsarin hada hada na MSCI, tun daga 1 ga watan Yuni dake tafe. Hakan a cewar Mr. Ulrich zai daga matsayin kasuwar hannayen jarin kasar zuwa matsayi na kasa da kasa.

Ya ce matakin zai jawo hankulan masu zuba jari kan kasuwar kasar Sin ta yadda yawan jari a rukunin hannayen jari rukunin A na kasar zai kai ga dalar Amurka biliyan 40. A daya hannun kuma, sauyin alkibla da tattalin arzikin kasar Sin ya samu zuwa samar da ci gaba mai inganci zai kara karfafa gwiwar masu zuba jari a kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China