Wani jami'in kwamitin aiwatar da kwaskwarima da raya kasa na kasar Sin ya bayyana a yau Alhamis 19 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin za ta rage wasu kudade da kamfanoni ke biya wadanda ba na haraji ba a wannan shekara, kuma adadin su ya wuce RMB biliyan 300, matakin da zai rage matsin lamba kamfanoni ke fuskanta, hakan za su iya mai da hankali kan neman bunkasuwa.
A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, wannan jami'in ya ce, a shekarun baya bayan nan, hukumomin raya kasa da yin kwaskwarima, suna kokarin daidaita tsarin tattara kudade daga kamfanonin da rage nauyin dake kan wuyan kamfanoni, inda aka samu ci gaba sosai a wannan fannonin.
Shugaban sashi mai kula da farashin kayayyaki na kwamitin Mista Yue Xiuhu, ya ce a cikin shekarar 2016 da 2017, an rage kudaden da kamfannoni suka biya da yawansu ya wuce RMB biliyan 500 ta hanyar daukar matakai na rage kudaden ba da hidima a fannonin da suka shafi hada-hadar kudi, da cinikayyar shige da fice da dai sauransu. (Amina Xu)