Masu zuba jari na cikin gida sun samar da kudi kimanin dalar Amurka biliyan 25.5 na jarin ODI a wasu kamfanoni kimanin 2,023 dake kasashen duniya da yankuna na duniya kimanin 140 tsakanin watannin Janairu zuwa Maris, kamar yadda ma'aikatar ciniki ta kasar Sin (MOC) ta tabbatar da hakan.
Alkaluman sun karu da kashi 24.1 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin a bara, in ji MOC.
Jarin na ODI a kasashen dake kan hanyar "ziri daya da hanya daya" ya ci gaba da samun bunkasuwa, inda ya samu karuwar kashi 22.4 bisa 100 a cikin shekara guda, wanda a baya adadin jarin dala biliyan 3.61 ne aka samu a watanni ukun farko na shekara.
Ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta wallafa a shafinta na intanet cewa, hannayen jarin sun shafi bangarori da dama, sai dai sun fi mayar da hankali ne a bangarorin da suka hada da bayar da haya, ma'adanai, masana'antu, da ayyukan da suka shafi fasahar sadarwa ta zamani.
Jarin ODI na kasar Sin yana matukar samun bunkasuwa cikin sauri a 'yan shekarun nan. Sai dai kuma, hukumomi suna cigaba da bada shawarwari ga kamfanoni da masu zuba jarin dasu kasance masu yin taka tsantsan wajen yanke shawara game da batun zuba jari. (Ahmad Fagam)