Kwamitin sa ido kan kaddarorin kasa na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya sanar a yau Litinin a nan birnin Beijing cewa, yawan kudin shiga da manyan kamfanonin dake karkashin mallakar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin suka samu ya kai RMB yuan biliyan 6400 a cikin watannin ukun farko na bana, wanda ya karu da kashi 8.7 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Mataimakin babban sakataren kwamitin Peng Huagang ya ce, a cikin watannin Jarairu, da Fabrairu da kuma watan Maris, yawan kudin da wadannan kamfanoni suka samu ya yi matukar karuwa, musamman ma a fanonnin samar da wutar lantarki da kwal da injuna da kauwanci da cinikayya da dai sauransu, yayin da a fannonin man fetur, gine-gine, sufuri da sauransu sun samu karuwa yadda ya kamata.
Ban da wannan kuma, an ba da labari cewa, a cikin wadannan watanni uku, yawan ribar da kamfanonin suka samu ya kai yuan biliyan 377 wanda ya karu da kashi 20.9 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. Daga cikinsu kuma, a watan Maris wannan adadi ya kai biliyan 169.87 wanda ya kai sabon matsayi. (Amina Xu)