Kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya ce jimilar sayayyar da aka yi cikin watanni ukun farkon shekarar nan, ya kai yuan trilian 1.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 238.5, adadin da ya karu kan na bara da kaso 34.4 cikin dari.
Ci gaban da bangaren ya samu ya dara sosai kan na kananan da manyan kantunan sayar da kayayyakin, duk da cewa su ma sun samu ci gaba sosai a bana.
Adadin sayayyar kayayyakin amfani ya karu da kaso 9.8 cikin dari a kan na bara wanda ya kai yuan triliyan 9 cikin rubu'in farko na bana.
Adadin ya dan karu ne kadan kan kaso 9.7 cikin dari da aka samu cikin watanni biyun farko,inda a watan Maris ya hau zuwa kaso 10.1 cikin dari.
Kayayyakin da ake amfani da su sun zamo jigon ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, al'amarin da ya bada gudunmawa ga habakar tattalin arzikin kasar da kaso 77.8 cikin dari a rubu'in farko, adadin da ya karu kan kaso 58.8 cikin dari na bara. (Fa'iza Mustapha)