Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce manufar kariyar cinikayya da Amurka ta kuduri aniyar aiwatarwa, za ta lahanta tattalin arzikin duniya baki daya ba wai kasar Sin kadai ba.
Hua ta bayyana hakan ne a Litinin din nan, bayan da ministan harkokin wajen kasar Australia Julie Bishop ya bayyana damuwa, game da matakin Amurka na kara haraji kan wasu hajoji, da wasu kasashe ke shigarwa kasar.
Da take maida martani bayan da aka bukaci ta yi tsokaci kan kalaman na Mr. Bishop, Hua ta ce wannan batu ne da ya shafi kasa da kasa, kuma kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya, wajen nuna adawa da wariya, tare da kariyar cinikayya. Tana kuma fatan kasashen duniya za su bude kofofin su, domin gudanar da cudanyar kasuwanci bisa doka.(Saminu Alhassan)