Cikin bayanin, WTO ta kuma bayyana cewa, ko da kasar Amurka ba ta yarda da bukatun da kasar Sin ta gabatarwa kungiyar ba, amma, tana son yin shawarwari kan batutuwan.
Dangane da matakin da kasar Amurka ta dauka bisa sashe na 232 na dokarta wajen kara haraji kan kayayyakin karfe da samholo da ta shigo da su daga ketare, kasar Amurka ta bayyana cewa, an dauki matakin ne ba domin kariyar ciniki ba, sai hana shigowar kayayyakin karfe da samholo wadanda suka kawo barazana ga tsaron kasar ta Amurka. Haka kuma, tana ganin cewa, tsarin WTO wajen warware sabanin ciniki a tsakanin kasa da kasa, ba zai taimaka wajen warware matsalar kudin kwastan dake shafar tsaron wata kasa ba.
Amma, kasar Amurka ta bayyana cewa, tana son yin shawarwari kan batutuwan dake shafar bincike kan sashe na 301 na dokarta da ta yiwa kasar Sin, amma ya zuwa yanzu, ba a fara aiwatar da matakan kara harajin a hukumance ba, shi ya sa, babu bukatar a warware matsalolin da kasar Sin ta gabatarwa kungiyar, bisa tsarinta na warware sabanin ciniki. (Maryam)