Haka kuma, ya ce, Sin da Amurka suna da bambanci kwarai da gaske a fannoni daban daban, kamar tarihi, al'adu, tsarin siyasa da kuma matsayin samun ci gaba da dai sauransu, ya ce wannan ba abin mamaki ba ne, amma ya kamata a nuna girmamawa da fahimta kan bambancin dake tsakanin kasashen biyu. Kasar Sin ba za ta yi hakuri kan ko wane batu dake shafar kare ikon kanta da kuma kiyaye cikakken zaman yankunan kasar ba, kana, ana fatan za a karfafa shawarwarin dake tsakanin bangarorin biyu kan harkokin ciniki, bisa ka'idojin girmama juna da adalci, ta yadda za a warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata da kuma cimma moriyar juna.
Haka zalika, ya ce, yadda dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka za ta ci gaba, ta danganta sosai kan yadda kasashen biyu suke fahimtar huldar dake tsakaninsu. (Maryam)