A cewar jami'an da suka tsara shirin, kimanin kamfanonin kasar Sin 4,000 ne suka gudanar da hada-hadar fitar da hajojinsu ketare wanda ya zarta kudin dalar Amurka biliyan 2.3 a lokacin bikin baje-kolin na wannan shekara, wanda aka kammala shi a ranar Lahadin da ta gabata.
Kayayyakin da kamfanonin kasar Sin suka fitar zuwa nahiyar Asiya ya karu da kashi 14.3 bisa 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda adadin ya kai dala biliyan 1.5, kuma baki daya an yi hada-hadar kashi 65 bisa 100 ke nan.
Sama da 'yan kasuwa 22,000 daga kasashen duniya da yankuna 109 ne suka halarci bikin baje-kolin, wanda ya kai girman murabbin mita 123,600. (Ahmad Fagam)