Madam Hua ta bayyana cewa, Sin tana bin ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, da tabbatar da tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, mai bude kofa ga kowa, da adalci, da hadin gwiwa bisa tushen kungiyar WTO da ka'idojin ciniki. Kaza lika Sin tana fatan warware matsalar da ake fuskanta, ta hanyar yin shawarwari bisa ka'idojin nuna girmamawa da adalci ga juna, da samun moriyar juna, ciki har da rikicin ciniki. Ta ce alal hakika, Sin da Amurka suna gudanar da shawarwari kan batutuwan tattalin arziki da na cinikayya.
Madam Hua ta jaddada cewa, Sin ta yi imanin cewa, tana da karfin tabbatar da iko da moriyar ta yadda ya kamata a ko wane irin hali. Har ila yau Sin tana fatan kasar Amurka za ta yi la'akari sosai, da tsaida kuduri wanda ya dace. (Zainab)