Mataimakin firaministan Sin ya zanta da sakataren kudin Amurka ta wayar tarho
Mamban ofishin siyasar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma mataimakin firaministan kasar Liu He,ya zanta da sakataren kudin Amuka, Steven Terner Mnuchin ta wayar tarho a yau Asabar, inda Mnuchin ya sanar wa kasar Sin sabon ci gaban da aka samu game da rahoton bincike mai lamba 301 da Amurka ta bayar. Liu He ya bayyana cewa, wannan rahoton da kasar Amurka ta gabatar, ya saba wa dokokin cinikayyar kasa da kasa, kuma ba zai amfanawa moriyar kasar Sin da Amurkar, har ma da moriyar duniya baki daya ba. Ya ce kasar Sin a shirye take, kuma tana da karfin kiyaye moriyarta, sannan ta na fatan bangarorin biyu za su yi tunani sosai, gami da kokari tare da nufin kiyaye dangantakar dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata. A yayin zantawar, bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tuntubar juna kan wannan batu. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku