Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira ga daukacin sassan dake da ruwa da tsaki game da batun zirin koriya, da su martaba kudurorin MDD game da batun zirin, da ma al'amura masu alaka da koriya ta Arewa.
Mr. Wang wanda ke amsa tambayoyin manema labarai a Litinin din nan, jim kadan bayan ganawar sa da takwaransa na Mongolia Damdin Tsogtbaatar, ya ce bayan watanni biyu kacal da samun daidaito a zirin na koriya, yanzu haka al'amura sun sake ta'azzara, kuma Sin na matukar takaicin ganin sassan da batun ya shafa, sun ki amincewa da shawarar da ta gabatar.
Wang Yi na amsa tambaya ne game da tambayar da aka yi masa, game da tasirin matakin da Amurka ta dauka, don gane da kakabawa Koriya ta Arewa karin takunkumi, bayan gwajin makami mai linzami na baya bayan nan da kasar ta yi.
Ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya ce, burin kasar sa shi ne barin kofar tattaunawa a bude, kuma ya dace a rungumi kudurorin MDD, da na kwamitin tsaron MDD dake matsayin madogara ga dukkanin sassa.
Wadannan kudurori a cewar Mr. Wang, su ne matsaya ta kasashen duniya baki daya.(Saminu Alhassan)