Jiya Jumma'a shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, kasarsa za ta yi wa kasar Koriya ta Arewa tukunkumi mafi tsanani kan tarihi. Ma'aikatar baitulmalin kasar ita ma ta sanar da cewa, za ta aiwatar da takunkumi ga wasu kamfanoni da wani mutum dake goyon bayan kasar ta Koriya ta Arewa, domin hana su samar da kudin da kasar take bukata wajen kera makaman nukiiya.
Trump ya fadi haka ne yayin da yake gabatar da wani jawabi ga masu sassaucin ra'ayi a gun taron da suka kira.
Daga baya ma'aikatar baitulmalin kasar ta sanar da cewa, za ta yi takunkumi ga kamfanonin ciniki da na jigilar kayayyaki ta hanyar jiragen ruwa da yawansu ya kai 27 da jiragen ruwa 28 da kuma wani mutum, ban da haka kuma, ma'aikatar baitulmalin kasar da majalisar zartaswar kasar da rundunar kiyaye tsaron gabar tekun kasar sun bayar da wata sanarwa game da jigilar kayayyaki kan teku a fadin duniya cikin hadin gwiwa, inda suka yi kashedi cewa, idan an ci gaba da gudanar da cinikin kayayyaki da Koriya ta Arewa ta hanyar jigilar kayayyaki kan teku, za a yi musu takunkumi.
A cikin sanarwar, ma'aikatar baitulmalin kasar ta bayyana cewa, makasudin daukar matakin shi ne domin hana a samar da taimako ba bisa ka'ida ba ga kasar ta Koriya ta Arewa.
Bisa tanadin da aka tsara, wadanda ake yi musu takunkumi ba za su iya yin amfani da kudinsu a kasar Amurka ba, haka kuma ba za su iya gudanar da ciniki da 'yan asalin kasar Amurka ba.(Jamila)