in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An mika wasikar shugaban Koriya ta Arewa ga shugaban Koriya ta Kudu
2018-02-11 12:38:51 cri

Jiya Asabar 10 ga wata, manzon musamman na shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un, kuma mataimakin minista na farko na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwadago wato Labor ta kasar Kim Yo-jong ya mikawa shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in wata wasikar da shugaba Kim Yong Un ya rubuta da hannunsa, inda Kim Jong Un ya bayyana cewa, yana fatan huldar dake tsakanin kasashen biyu za ta kyautata, kana ya gabatar da gayyata ga shugaba Moon Jae-in da ya kai ziyara kasar ta Koriya ta Arewa.

A jiya Asabar a Cheon Wa Dae, fadar shugaban kasar ta Koriya ta Kudu, Moon Jae-in ya yi ganawa da tawagar manyan wakilan kasar ta Korea ta Arewa wadanda ke ziyara a kasarsa, kuma sun ci abincin rana tare.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya, kakakin fadar Cheon Wa Dae Kim Eui-kyeom ya bayyana cewa, a madadin Kim Jong Un, Kim Yo-jong ya gayyaci Moon Jae-in da ya kai ziyara a Koriya ta Arewa a lokacin da ya dace, kuma ya bayyana cewa, shugaba Kim Jong Un yana fatan zai yi ganawa da shugaba Moon Jae-in cikin sauri.

A nasa bangaren, shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya bayyana cewa, yana fatan zai kai ziyara a Koriya ta Arewa da zarar ya yanke shawara, kana shi ma ya yarda cewa, idan sassan biyu wato Koriya ta Kudu da ta Arewa suna son kyautata huldar dake tsakaninsu, ya zama wajibi Koriya ta Arewa da kasar Amurka su gudanar da shawarwari tun da wur wuri, a don haka yana fatan Koriya ta Arewa za ta nuna kwazo da himma domin gudanar da shawarwari dake tsakaninta da kasar ta Amurka.

Wannan ne karo na farko da Koriya ta Arewa ta tura tawagar manyan jami'anta zuwa ga Koriya ta Kudu tun bayan da ta tura irin wannan tawagar domin halartar bikin rufe gasar wasannain motsa jiki ta kasashen Asiya a birnin Incheon a shekarar 2014.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China