Ma'aikatar kudin Amurka, ta sanya wasu sabbin takunkumai kan wasu mutane 7 da wasu kadarori 3 na Jamhuriyar Demokradiyyar Al'ummar Koriya, bisa dalilan da ta kira da take hakkin dan Adam.
Sakataren ma'aikatar Steven Mnuchin, ya ce takunkuman sun shafi wasu jami'an rundunar sojin kasar dake da hannu wajen take hakkin bil'adama da masu samar wa Pyongyang kudade ta hanyar ci da gumin mutane.
Daga cikin daidaikun mutanen da aka kakabawa takunkuman, akwai jami'an soji da ministan kwadago Jong Yong Su da wakilin kasar a yankin Shenyang na kasar Sin da kuma wani jam'in ofishin jakadancin kasar dake Vietnam. (Fa'iza Mustapha)