A yayin da suke halartar taron shekara-shekara na asusun inganta sha'anin hanyoyin mota na Afrika (ARMFA) a Addis Ababa, na kasar Habasha, tsakanin ranakun 19 zuwa 23 ga watan Fabrairu, kwararru a fannin titunan mota da masana tsara dabarun mulki sun jaddada muhimmancin bunkasa fannin titunan mota domin samun kwakkwaran cigaba, inda kuma suka bada fifiko game da matakan da ya kamata a dauka wajen kulawa da ingancin titinan mota da kiyaye su yadda ya kamata.
Rashid Mohammed, shi ne shugaban ARMFA, ya shedawa mahalarta taron cewa, mayar da hankali wajen kyautata cigaban titunan mota wani muhimmin ginshiki ne da zai tabbatar da cigaban tattalin arzikin Afrika.
A cewar Mohammed, rashin kulawa da titunan mota yadda ya kamata da rashin samun damar amfani da wasu daga cikin titunan motar sun kasance a matsayin manyan kalubaloli dake damun manoman yankunan karkara a mafi yawan kasashen na Afrika inda hakan ke hana su damar cin gajiyar amfanin gonar da suka noma yadda ya kamata.
"Samun dawwamamman cigaban tattalin arzikin Afrika ya dogara ne da ingantuwar titunan mota a nahiyar, da kuma kula da titunan da kiyaye su," inji Mohammed.
Shugaban hukumar kula da titunan ta kasa da kasa (IRF), Kiran Kapila, ya jaddada muhimmancin daukar matakan inganta fannin titunan mota a nahiyar domin samun bunkasuwa, wanda hakan yana da alaka da shirin ajandar cigaban Afrika nan da shekarar 2063, wanda kungiyar tarayyar Afrika AU ta tsara.(Ahmad Fagam)