A jiya Laraba ne kwararru da masana a fannin kiwon tsuntsaye na kasa da kasa suka gana a birnin Kigalin kasar Rwandan, domin tattauna hanyoyin hana yaduwar cututtukan dake kashe tsuntsaye a nahiyar Afirka.
Taron na kwanaki biyu wanda ake fatan kammala shi a yau Alhamis, zai baiwa kwararru da masu zuba jari a wannan fanni da kanana da manyan masu kiwon tsuntsaye damar musayar ilimi da sabbin fasahohi game da hanyoyin hana yaduwar cututtukan dake halaka tsuntsaye
Tsohon shugaban kungiyar masu kiwon tsuntsaye na kasa da kasa(WPSA) Edir Silva ya ce, barkewar cututtukan dake halaka tsuntsaye kamar cutar murar tsuntsaye ta baya-bayan nan, ta yi mummunar illa ga gonakin dake kiwon kaji a nahiyar Afirka.
A don haka, ya ce akwai bukatar wadanda wannan lamari ya shafa su bullo da managartan matakan hana yaduwar irin wadannan cututtuka dake halaka tsuntsaye, kara samar da taimakon kudi, kana a zauna cikin shiri tare da bullo da matakan tinkarar lamarin a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.
Alkaluman hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD, na nuna cewa, a wannan shekara an samu bullar cutar murar tsuntsaye a kasashen Burkina Faso, da Kamaru, da Cote I'Ivoire, da Ghana, da Nijar. Sauran sun hada da Togo, da Najeriya da Jamhuriyar demokiradiyar Congo, da Afirka ta kudu, da Uganda, da kuma Zimbabwe
Taron na Kigali zai mayar da hankali ne kan samar da yanayin cinikayya tsakanin kwararru a wannan harka dake kasashen yankin Afirka dake kudu da hamadar Sahara da masu kiwon tsuntsaye da kamfanonin dake samar da tsuntsaye da kwai. Taken taron na birnin Kigali, shi ne, "Baje kolin tsuntsaye na Afirka na shekarar 2017". (Ibrahim)