Daraktan cinikayya na Kasuwar bai daya ta yankin gasbashi da kudancin Afrika wato COMESA, Francis Mangeni ya bayyana cikin jawabinsa da aka wallafa jiya a jaridar The Star ta kasar Kenya cewa, kawo yanzu, kasashe 19 daga cikin kasashe 26 dake cikin shirin ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Yankin cinikin cikin 'yanci zai samar da kayayyaki dari bisa dari ba tare da haraji ba na tsawon shekaru 5-8, sai dai kuma, bayan kula yarjejeniyar za a kara cin gajiyar rangwamen harajin da ya kai kashi 60-85 cikin 100. (Fa'iza Mustapha)