Yayin wani taro kan samarwa da rarraba lantarki da ya gudana a Johannesburg, Lynne Brown ta ce nan ba da dadewa ba, gwamnati za ta gabatar da sabon tsarin da za ta yi amfani da shi, wanda zai kunshi abun da take da niyyar aiwatarwa da kuma yadda za ta aiwatar.
Ministar ta ce suna sane da cewa, tsarin na bukatar janyewa daga dogaro da kwal tare da rungumar sabon tsarin hadin makamashi da ya kunshi Kwal da iskar gas da nukiliya da sauran wadanda ake iya sabuntawa, ta na mai cewa tuni kamfanin Eskom mai samar da lantarki a kasar ya fara aiki da nufin rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli daga tasoshin makamashinsa na kwal.
Afrika ta kudu ta shiga wasu yarjeniyoyin da kasashen duniya, kamar yarjejeniyar Paris ta 2016 wadda ta nemi kasar ta rage gurbataccen hayaki da take fitarwa.
Yanzu haka, kasar ta mai da hankali ga samar da makamashi daga albarkatun sassan nahiyar tare da kyautata rayuwar matalauta da marasa galihu a cikin al'ummar ta. (Fa'iza Mustapha)