Rahoton alkaluman ci gaban zamantakewar al'umma da aka kaddamar jiya a Ghana, ya ce sakamako daga yankin ya nuna cewa, duk da habakar tattalin arziki cikin shekaru 20 da suka gabata tsakanin 1992 da 2013, har yanzu kasashe na fuskantar kalubalen samun ci gaba bisa daidaito da tafiya tare da kowa.
Rahoton wanda aka shirya bisa nazartar kasashe 8 daga cikin 16 na kasashen yammacin Afrika, ya bayyana fatara a matsayin abun da ke hana shigar da jama'a cikin al'amura a dukkan kasashen, yayin da rashin ilimi ke zama babban gudunmuwa ga matsalar a akalla kasashe 5.
A rahotonta na 2016, hukumar ECA ta ce bukatun gaggawa da galibin kasashen yammacin Afrika suka fuskanta, misali barkewar cutar Ebola a shekarar2014, ya yi mummunan tasiri akan farashin abinci da kudaden shiga na iyalai da ake warewa harkokin ilimi.
Rahoton ya ce nazarin ya tabbatar da wasu fitattatun manufofin yankin na ciyar da ilimi gaba. (Fa'iza Mustapha)