Mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang, ya gana a jiya Jumma'a ta wayar tarho da sakataren harkokin cinikayya na Amurka.
Jami'an biyu sun yi zuzzurfar tattaunawa kan shirye-shiryen sakamakon harkokin tattalin arziki da ake hasashen samu yayin ziyarar da Shugaban Amurka Donald Trump zai kawo kasar Sin, tare kuma da sauran wasu batutuwan dake da alaka da huldar cinikayya da tattalin arziki dake tsakanin Kasar Sin da Amurka.
Ana sa ran Shugaba Donald Trump zai kawo ziyara kasar Sin a watan gobe, a wani bangare na ziyarar da zai kai kasashe 5 na nahiyar Asiya da suka hada da Japan da Koriya ta Kudu da Vietnam da Philippines. (Fa'iza Mustapha)