Yau Laraba ne madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar Sin ta yi tir da yadda wata babbar mota ta bi ta kan mutane da kuma yin harbe-harbe a birnin New York na kasar Amurka. Ta'addanci, abokin gaban dan Adam ne. Haka kuma kasar Sin ba ta goyon bayan duk wani nau'i na ta'addanci. Tana kuma karfafa hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen yaki da 'yan ta'adda.
A jiya ne, wata babbar mota ta bi ta kan mutane tare da yin harbe-harbe a unguwar Manhattan dake birnin New York na Amurka, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 8, tare da raunata wasu 11. Yanzu haka dai an kama wanda ya aikata wannan danyen aiki. Magajin garin birnin New York Bill de Blasio ya bayyana cewa, akwai shaidu dake nuna cewa, hari ne na ta'addanci. (Tasallah Yuan)