A yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin na fatan ziyarar da shugaba Donald Trump na kasar Amurka zai kawo kasar Sin za ta kara kyautata hadin gwiwa da moriyar juna a tsakanin Sin da Amurka, tare da kara kawo wa jama'ar kasashen 2 alheri, da kuma kara ba da gudummowa wajen samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya.
Nan ba da dadewa ba ne ake sa ran, shugaba Donald Trump na Amurka zai kawo ziyara kasar Sin, bisa gayyatar takwaransa na kasar Sin Xi Jinping. (Tasallah Yuan)