Shugaba Moon Jae-in ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin biki na 17, na sake zagayowar ranar 15 ga watan Yuni, ranar da sassan biyu suka sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a birnin Pyongyang, karkashin jagorancin shugaban Koriya ta Kudu na lokacin Kim Dae-jung, da takwaran sa na Koriya ta Arewa Kim Jong Il.
Ya ce idan har Koriya ta Arewa ta amince da batun dakatar da gwajin makamai masu linzami, ko shakka babu hakan zai tallafa matuka, wajen cimma nasarar waccan yarjejeniya da aka amince da ita a baya, kuma kasar sa za ta bada cikakken goyon bayan ta.
Shugaba Moon ya kara da cewa, kasashen biyu za su iya tattaunawa tsakanin su, game da muhimman batutuwa da suka hada da kauda makaman nukiliya daga Koriya ta Arewa, da kafa yanki mai cike da zaman lafiya a zirin Koriya, tare da tallafawa wajen maido da kyakkyawar huldar diflomasiyya tsakanin Koriya ta Arewa da kasar Amurka. (Saminu)