Geng ya ce, mahukuntan kasar Sin suna sane da wannan labari, kuma bisa iya saninsu, lamarin ya faru ne a kasar Malaysia, a saboda haka, mahukuntan kasar ta Malaysia suna gudanar da bincike game da wannan lamari.
Ofishin jakadancin kasar Koriya ta arewa dake Malaysia ya tabbatar da cewa mutumin dan shekaru 46 da haihuwa, wanda ke rike da fasfo da sunan Kim Chol, a hakika shi ne dai Kim Jong Nam.
Tuni kuma wasu kafofin kasar suka rawaito mataimakin firaministan kasar ta Malaysia Ahmad Zahid Hamidi na tabbatar da hakan. (Saminu)