Rahoton Kamfanin dillancin labaran ya ce, Amurka ta dorawa Koriya ta Arewa alhakin rashin nasarar tattaunawa a tsakaninsu, saboda Amurkan na son kakabawa Koriya ta Arewa takunkumin tattalin arziki tare da matsa mata lamba ta fuskar daukar matakan soji.
Ya kara da cewa, Amurka ba ta da kyakkyawar fata ga tattaunawa da Koriya ta Arewa, inda ta dauki matakan soji a kanta, da hana ta samun ci gaba, tare kuma da kakaba mata takunkumin tattalin arziki, da girke makaman nukiliya a kasar Koriya ta Kudu.
Har ila yau, rahoton Kamfanin ya ruwaito cewa, muddin shugaban Amurka Donald Trump bai yi watsi da manufarsa ta nuna kyamar Koriya ta Arewa ba, to ko kadan, Koriya ta Arewa ba za ta yi sha'awar tattaunawa da Amurka ba.(Murtala Zhang)