Geng ya ce, mahukuntan kasar Sin suna sane da wannan labari, kuma bisa iya saninsu, lamarin ya faru ne a kasar Malaysia, a saboda haka, mahukuntan kasar ta Malaysia suna gudanar da bincike game da wannan lamari.
Rahotanni na cewa, a ranar Litinin ne aka samu Kim Jong Nam, babban yaya ga shugaban kasar Koriya ta Arewa a mace a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia.
Rundunar 'yan sandan kasar Malaysia ta bayyana cewa, ta kama wata mace a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke Kuala Lumpur, yayin da Kim Jong Nam din ya bukaci taimako saboda rashin jin dadin jikinsa. Amma daga bisani ya mutu a kan hanyar kai shi asibiti.(Ibrahim)