Rahoton da kamfanin Moody mai nazarin harkokin kudi ya fitar a jiya Litinin, ya bayyana kasashen a matsayin wadanda ba su da yawan hannayen jari, kuma suka dogara kan jari kalilan da suke samu, inda ya bayyana kasashe 36 da suka shiga suka fada rukunin.
Rahoton ya ce kasashen su ne wadanda suka dogara a kan shigar da kayayyaki daga wasu kasashe da rashin isasshen tsarin harkokin kudi da kuma yawan bukatar bashi.
A cewar rahoton, matsalar za ta fi shafar kasashen Masar da Pakistan da Mongolia.
Ya kara da cewa, zuba jari kai tsaye na kasar Sin ya zama wani muhimmin abu ga wadancan kasashe, inda 16 daga ciki suka kasance karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya" na kasar Sin.
Kamfanin Moody ya ce jarin kasar Sin zai taimaka wajen magance hadarin da za a iya fuskanta a nan kusa. (Fa'iza Mustapha)