Hakan ya kasance karo na biyu da bankin AIIB ya samu cimma wannan matsayi na amincewa cikin rabin wata.
Cikin sanarwarsa, kamfanin Fitch Ratings ya ce, ya ba bankin AIIB wannan matsayi ne bisa la'akari da fifikon da bankin ke da shi, musamman ma a fannin makudan kudin da aka kebewa bankin. A cewar kamfanin Fitch Ratings, kudin da bankin ke samu zai taimakawa habakar rancen da take samarwa. Ban da haka kuma, wasu matakai masu kyau da ake dauka a fannin kula da bankin zai taimakawa rage yiwuwar fuskantar hadari a nan gaba.
Yawan kudin da aka zubawa bankin AIIB ya kai dalar Amurka biliyan 100. Tun da aka kafa bankin a watan Janariun shekarar 2016, mambobin da suka zuba jari ga bankin na ta karuwa, kana bankin ya riga ya yarda da zuba jari ga manyan ayyukan gina kayayyakin more rayuwa 16, inda ya ware kudin da ya kai dalar Amurka bilian 2.5.(Bello Wang)