Matakin kamfanin na MSCI na kara manyan kasuwannin hannayen jarin kasar Sin 222, ya nuna karuwa ta a kalla kaso 0.73 cikin 100 na karfin kasuwannin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa zuwa kaso 5 cikin 100 na kamfanonin hannayen jarin da suka samu shiga kamfanin na MCSI, kamar yadda ya ke kunshe cikin rahoton fasalin kasuwar kamfanin na shekarar 2017.
MSCI ya ce, wannan shawara ta samu goyon bayan cibiyoyin harkokin zuba jari na kasa da kasa, biyo bayan tasirin saukin kaiwa ga manyan kasuwanni da shirye-shiryen hannayen jarin kasar da saukaka musayar ka'idojojin da suka shafi hannayen jari suka haifar ,wadanda za su iya kawo cikas ga kokarin kirkiro hanyoyin sanin alkaluman da suka shafi kudaden da aka adana na duniya.(Ibrahim)