Rahoton hukumar ya nuna cewa, duniya ta samu ci gaban kaso 3.5 cikin 100 a wannan shekarar ta 2017 inda aka samu karin kaso 0.2 cikin 100. Ana kuma hasashen ci gaba a shekarar 2018 mai zuwa zai kai kaso 3.6 cikin 100 sakamakon tabbacin da ake da shi a kan harkokin kasuwanci da na masu sayan kayayyaki, da karuwar kayayyakin da masana'antu ke samarwa da karuwar guraben ayyukan yi da kuma bunkasuwar harkokin cinikayya.
Babban sakataren hukumar Angel Gurria ya bayyanan cewa, bayan shekaru biyar da aka shafe ana fama da koma baya ta fannin ci gaba, akwai alamomin ci gaba a wannan fanni. Sai dai kananan ci gaban da aka samu ba za su wadatar ga dorewar nasarori da aka samu a fannonin rayuwa a kasashen mambobin hukumar ba.
A saboda haka Guriia ya ba da shawarar ci gaba da hada karfi da karfe da bullo da managartan manufofi da za su tallafawa ci gaban da aka samu, don tabbatar da cewa, fa'idodin farfadowar tattalin arzikin duniya da aka samu sun yi tasiri a kokarin da ake yi na inganta harkokin rayuwar al'ummma. (Ibrahim Yaya)