Rahoton binciken farfado da tattalin arzikin duniyar da aka gabatar ya shaida cewa, kasashe masu ci gaban tattalin arziki suna bin hanyar bunkasuwar tattalin arziki mai dacewa, da sassauta faduwar farashin kaya. Ana kyautata yanayin sabbin kasashe mafi samun bunkasuwar tattalin arziki, yawan bunkasuwar tattalin arzikinsu a bara ya taba yin kasa da na mafi karancin yawansu a da, yanzu ya riga ya karu zuwa matsayin koli bayan shekarar 2013.
Shugabar asusun bada lamuni na duniya Christine Lagarde, ta bayyana a kwanakin baya cewa, ana kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya, farfadowar tattalin arzikin za ta samar da kyakkyawan fata a fannonin samar da aikin yi, karuwar kudin shiga, samun wadata da sauransu. (Zainab)