in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta dukufa wajen hana barkewar yakin makaman nukiliya tsakaninta da Koriya ta Arewa
2017-09-25 13:29:46 cri
Ministan harkokin kudin kasar Amurka Steven Terner Mnuchin ya bayyana a jiya cewa, shugaban kasar Amurka zai dukufa wajen hana barkewar yakin makaman nukiliya tsakanin kasar sa da kasar Koriya ta Arewa.

Ya kuma kara da cewa, matakan da shugaban kasar Donald Trump ya dauka a kwanan baya sun nuna cewa, zai dauki dukkan irin matakai na tattalin arziki, da na soja, domin warware matsalar kasar Koriya ta Arewa.

A sa'i daya kuma, ya ce, shugaba Trump ba ya fatan shigar da kasar Amurka cikin wani yaki na makaman nukiliya, don haka ne ma, za a dukufa wajen hana duk wani yanayi da ka iya haifar da barkewar yakin makaman nukiliya tsakanin kasar Amurka da Koriya ta Arewa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China