Mahukunatan na Japan su ka ce makamin ya sauka ne a nisan kilomita 2,000 gabas da yankin Erimo a Hokkaido da msalin karfe 7.16 na safe agogon Japan.
Harba wannan makami da Koriyar ta arewan ta yi, na zuwa ne bayan da kwamitin sulhun MDD ya kada kuri'ar amince da tsaurara wa kasar takunkumi, sakamakon gwaje-gwajen nukiliya a karo na shida da kasar ta yi a ranar 3 ga watan Satumba,.
Babban sakataren majalisar zartarwar kasar Japan Yoshihide Suga ya ce kasarsa ta yi allah wadai da kakkausar murya kan gwajin na baya-bayan, wanda ta bayyana a matsayin takalar fada.
Suga ya ce, makamin da Koriya ta arewan ta harba bai yiwa japan din wata illa ba. (Ibrahim)